Assalamu alikum masu sauraro barmammu da warhaka, sharhin bayan labarummu na yau zai magana ne kan ‘Hare-Haren maida martani na ‘Wa’adus Sadiq-II’ wanda dakarun IRGC na JMI suka y ikan HKI a daren Talatan da ta gabata, da kuma tasirinsa a yankin gabasa ta tsakiya da ma duniya gaba daya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare hare da makamai masu linzami ko kuma “Wa’adus Sadik II’ wanda JMI ta kaiwa HKI a ranar Talatan da ta gabata, yana bisa ka’ida, yana kuma bisa doka, kamar yadda ya zo a cikin kuduri mail amba 51 na MDD.
Bayan hare haren Aragchi ya zanta ta wayar Tarho da ministocin harkokin waje na kasashen Faransa, Burtania da kuma Jamus, inda ya bayyana masu korafe korafen JMI dangane da laifufukan yakin da HKI take aikatawa a cikin kasashen Asiya ta kudu, wadanda suka hada da kissan kare dangin da take yi a Gaza, da Lebanon da kuma wadanda ta aikata a nan Tehran da wasu wurare, wadanda suka hada da Yemen, Siriya da kuma Iraki.
Ministan ya kara da cewa “saboda haka ne JMI ta kai wadannan hare hare” kan cibiyoyin soje na HKI, Aragchi ya kara da cewa JMI bata son yaki da ko wace kasa a duniya, amma kuma ba ta jin tsoron yaki, idan an dora mata shi.
Idan kuma HKI ta yi kokarin ramawa kan JMI, hare hare masu zuwa kanta sai sun fi tsanani a kan na “wa’adussadik II”.
Daga karshe Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bukaci dukkan kasashen duniya su yi kokarin ganin an tsagaita budewa juna wuta, da kuma dakatar da hare haren da sojojin HKI suke kaiwa kan kasashen yankin musamman kan kasar Lebanon da kuma yankin zirin Gaza.
Har’ila yau ministan ya aika sako a shafinsa na X kan Internet ko yanar gizo, inda ya rubuta cewa, {JMI ta kai hare haren Wa’adus Sadik II} ne bayan hakuri na kimani watanni 2 ganin an dakatar da bude wuta a Gaza”.
Hakama Amir Sa’id Iravani, wakilin din din din kuma jakadan kasar Iran a MDD ya rubutawa babban sakaren MDD Antonio Goterres da kuma shugaban kwamitin Tsaro na MDD a cikin wannan watan Pascal Christian Bresville inda ya fada masu cewa hare haren JMI kan HKI yana bisa doka, kamar yadda yake a kuduri mail lamba 51 na MDD, wanda ya bawa JMI damar kare kanta da kuma maida martani idan wata kasa ta tsongometa.
A cikin wasikar Iravani ya kara da cewa: Sabanin hare haren da sojojin HKI suke kaiwa kan mutanen Gaza, da Lebanon, inda suke kashe fararen hula mata da yara gaba daya, JMI a hare haren ‘Wa’adus Sadik II’ ta rarraba tsakanin fararen hula da yara da kuma sojojin makiya. Ta takaita hare haren ta ne kan wuraren soje da kuma cibiyoyin tsaro da sauransu kadai.
Iravani ya kara da cewa, sojojin JMI sun kai hare haren Wa’adus Sadik II’ kan wuraren soje na HKI ne kadai, bayan dauriya na kimani watanni biyu da kashe Shahid Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas wacce take fafatawa da sojojin HKI a Gaza, sanan da kashe Shahid Sayyid Hassan Nasarallah shugaban kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon a ranar Jumma’an da ta gabata, da kuma kashe Janar Abbas Nilfurushan babban jami’a a cikin dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran, wanda kuma shi ne mai kula da al-amuran Lebanon a rununar ta IRGC, har’ila yau wanda ya kasance tare sayyid Hassan Nasarallah a lokacin da aka kai masa hari.
Har’ila yau da kashe mata da yara da fararen hula a Gaza da Lebanon. JMI yi amfani da wannan hakkin na ta na maida martani bisa dukkan wadannan al-amura, a ranar Talatan da ta gabata 01-10-2024, ta kai hare hare da makamai masu linzami kimani 400 kan cibiyoyin tsaro ko soje na HKI.
Hare haren maida martani na ‘Wa’adus Sadik II” dai ya farantawa mutane da dama rai, kama daga Falasdinawa a Gaza, mutane Lebanon, Iraki, Yemen, Syriya da kuma nan kasar Iran.
Da dama sun yi farin ciki da samun wanda zai ladabtar da HKI kan irin mummunan dabi’ar da take nunawa a kasashen yankin na kisa da rusa gine gine a kan masu su, a kasashen Lebanon, Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan na kasar Falasdinu da aka mamaye. Masu sauraro karshen sharbin bayan labaran kenan.