Shamkhani Ya Yi Gargadin Cewa: Takaita Wuraren Mayar Da Martanin Iran “Mafarki” Ne Na Marassa Zurfin Tunani

Shamkhani ya yi gargaɗi ga Amurka cewa: Takaita wuraren mayar da martanin Iran “mafarki ne,” kuma martanin zai kasance cikakke Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin

Shamkhani ya yi gargaɗi ga Amurka cewa: Takaita wuraren mayar da martanin Iran “mafarki ne,” kuma martanin zai kasance cikakke

Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Admiral Ali Shamkhani, ya tabbatar da cewa: Duk wani matakin soja na Amurka, ba tare da la’akari da girmansa ko dalilansa ba, zai zama farkon yaƙi mai girma. Ya jaddada cewa martanin Iran zai kasance nan take, cikakke, kuma ba a taɓa ganin irinsa ba, yana mai lura da cewa manufofinta za su kai ga zuciyar Tel Aviv da duk waɗanda ke goyon bayan duk wani hari da aka kai wa Iran.

A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X, Shamkhani ya rubuta cewa: “Mayar da martani iyakantacce, mafarki ne. Duk wani matakin soja da Amurka za ta ɗauka, daga kowane fanni da kuma a kowane mataki, za a ɗauke shi a matsayin farkon yaƙi, kuma martanin zai kasance nan take, cikakke, kuma ba a taɓa ganin irinsa ba, wanda zai kai ga zuciyar Tel Aviv da duk waɗanda ke goyon bayan mai kai harin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted