Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Admiral Ali Shamkhani da tashar talabijin din ‘almayadin’ tayi hira da shi ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka za ta takaita ne akan batun makamashin Nukiliya kadai.
Admiral Shamkhani ya ce; Shirin Iran na makamashin Nukiliya na zaman lafiya ne, don haka batun tace Uranium zuwa daraja 60%, za a iya rage shi zuwa 20% idan har wannan ne abinda yake damunsa,amma fa ba haka kawai za a yi ba, sai sun gabatar da wani abu.
Haka nan kuma Admiral ya ce, Iran ta kara darajar Uranium din da take tacewa ne, domin fuskantar makircin makiya, domin ya zama abinda za a yi tattaunawa akan shi.”
Wani sashe na bayanin Admiral Shamkhani ya kunshi cewa; ko kadan kasashen turai ba su fahimtar abinda muke fada na cewa; mallakar makaman Nukiliya haramun ne, don haka ba abu ne da za a iya sauya shi da wani umarni ba, saboda ya fito ne daga mahangar marja’i da shi ne jagoran juyin musulunci Sayyid Ali Khamnei.