Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta

Shaikh Naim Qasim babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar labanon ya bayyana cewa kisan babban kwamanda Haitham Ali tabataba’I da isra’ila ta yi

Shaikh Naim Qasim babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar labanon ya bayyana cewa kisan babban kwamanda Haitham Ali tabataba’I da isra’ila ta yi bai zai sa ta cimma manufofinta ba, don haka hizbulla za ta mayar da martani a lokacin da ya dace,

Wadanan kalaman suna zuwa ne a lokacin da ake zaman dar-dar tun bayan kisan gillan da isra’ila ta yi wa babban kwamandan hizbulla , kuma wani mataki ne kamar yadda shaikh naim Qasem ya bayyana ta yi kisan ne don karya bangaren soji na kungiyar sai dai hakarta ba za ta cimma ruwa ba,

Babban sakataren ya bayyana jin dadinsa game da sakonnin ta’azziya da aka aiko daga bangarorin shuwagabannin jam’iyun siyasa a ciki da wajen kasar, kuma ya mika godiya ta musamman ga kasar iran musamman jagoran juyin musulunci na kasar Ayatullah imam Khamanai,da ma sauran manyan jami’am gwamnatin kasar

Haka zalika yace yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan nuwambar shekara ta 2024 babbar nasara ce ga yan gwagwarmaya da ma alummar labanon ,yace isra’ila ta amince da yarjeejniyar ne saboda ta kasa yin galaba akan hizbullah, kana ya jinjinawa wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen ganin an samu nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments