Search
Close this search box.

Sayyid Nasrallah: Iran Ta Tabbatar Da Cewa A Tsaye Da Kafafunta Wajen Fuskantar Kowane Irin Kalubale

Babban magatakardar kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Hizbullah wanda aka watsa jawabinsa a wurin juyayin 40 na shahadar Sheikh Ibrahim Ra’isi ya ce; Iran ta sami

Babban magatakardar kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Hizbullah wanda aka watsa jawabinsa a wurin juyayin 40 na shahadar Sheikh Ibrahim Ra’isi ya ce; Iran ta sami mafita da abu maras dadi da ya faru da ita na shahidan hidima, ta kuma zama abin koyi na koli wajen fuskantar kalubale mai yawa.

Sayyid Nasrallah ya sake mika ta’aziyyar shahadar Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, a madadinsa da kuma kungiyarsa ta gwgawarmaya,ga jagoran juyin juya halin musulunci da manyan malaman addini da al’ummar Iran.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda miliyoyin mutanen Iran su ka halarci janaizar shugaban kasar ta Iran na 8 shahid Ibrahim Ra’isi tare da abokan tafiyarsa da hakan ya zama wani sako na musamman ga makiya da abokan jamhuiryar musulunci ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments