Sayyed Nasrallah Ya Ja Kunnen Isra’ila Kan Gigin Kai Hari Lebanon

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah ya yi gargadin cewa “babu wani wuri” a Isra’ila da zai tsira daga makamai masu linzami

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah ya yi gargadin cewa “babu wani wuri” a Isra’ila da zai tsira daga makamai masu linzami na kungiyarsa idan har shugabannin Isra’ila suka aiwatar da barazanar kai hari a Lebanon.

“Abokan gaba sun sani da kyau cewa mun shirya fiye da yadda ake zato, kuma sun san cewa babu wani wuri da zai tsira daga harin makamanmu masu linzami”

Hassan Nasrallah, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar kai tsaye ta gidan talabijin da yammacin yau Laraba.

Makiyanmu su san cewa a shirye muke ta ko ina, ta kasa, ta ruwa da kuma sama.

Shugaban kungiyar ta Hezbollah, Ya kuma yi barazana ga Cyprus idan har ta yanke shawarar bude filayen tashi da saukar jiragen saman ta da sansanoninta ga Isra’ila domin yaki da kungiyarsa.

“Bude filayen jirgin saman Cyprus da sansanonin ga abokan gaba na Isra’ila don kai hari kan Lebanon yana nufin cewa gwamnatin Cyprus ta shiga cikin yakin” Inji Hasssan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments