Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu
Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya.
Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na SPA cewa: Majalisar zartaswar kasar Saudiyya ta tattauna batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya da ma kasa da kasa.