A wani bincike wanda tashar talbijin din Aljazira Ta kasar Qatar ta gudanar ta hanyar bibiya, ta bayyana cewa sau 6000 jiragen sama na Amurka da kasashen turai su ka yi jigilar makamai zuwa Isra’ila domin taimaka mata da makaman da su ka rika jefa wa Gaza a tsawon shekara daya.
Bugu da kari, bayan gushewar shekara daya daga fara yaki da kisan kiyashi a Gaza,Amurka da kasashen na turai sun cigaba da kai wa HKI makamai kuma ba taimaka mata da bayanai na sirri ta hanyar jibge jiragen tattara bayanai akan ‘yan gwagwarmaya na Gaza da Lebanon.
Har ila yau cibiyar “ Sanad Lirrasad Wal Tahqiq” dake karkashin Aljazira ya bi dididgin bayanai na zirga-zirgar jiragen sama zuwa Isra’ila wanda ya fara tun daga ranar 7 ga Oktoba zuwa yanzu,da hakan ya sa ta gano dakon makamai da kayan yaki 1900 zuwa Isra’ila, da kawo 70% na Amruka ne da Birtaniya.
Birtaniya kuwa ita ce kasa ta biyu bayan Amurka wacce tata zirga-zirgar ta soja da makamai ta kai kaso 47% na jumillar 6000 da aka kai wa ‘yan sahayoniyar.