Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blibnken ya yi kira ga sabon shugaban kungiyar Hamas a bangaren siyasa Yahaya Sinwar da, wai ya dauki matakin tsagaita wuta a Gaza, ya kuma kawo abinda ya kira karshen yakin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Blinken yana fadar haka jim kadan bayan da kungiyar Hamas ta bada sanarwan zaben Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaban kungiyar a bangaren siyasa.
Blinken yana Magana kamar kungiyar Hamas ce taki amince a tsagaita wuta a gaza, bayan da ya san cewa HKI ce ta ki amincewa da tsagaita wutar. Don kungiyar Hamas ta amince da tsagaita wutar tun lokacinda kofin yarjeniyar ya shiga hannun marigayi Haniyya sai dai sun bukaci a sauya wasu wurare a cikinta.
Tun bayan kissan Haniyya a Tehran ne kungiyar ta jingine batun tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta masu shiga tsakani.
A wani bangaren kuma Blinken ya bayyana cewa Amurka tare da masu shiga tsakani sun aikewa Iran da kuma HKI kan cewa kada a fadada yakin na Gaza. Wannan na zuwa ne bayan kissan da sojojin HKI suka yiwa shugaban Hamas a Tehran da kuma ci gaba da kissan Falasdinawa a gaza.
Iran dai tace zata dauki fansar kissan Haniyya a Tehran, kuma ba zata saurari wadanda suke hanata yin hakan ba.