SADC: Fari a Kudancin Afirka yana shafar mutane kusan miliyan 68

Kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta SADC ta sanar da cewa, sakamakon fari da ake fama da shi a kudancin Afirka, hakan ya haddasa matsaloli

Kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta SADC ta sanar da cewa, sakamakon fari da ake fama da shi a kudancin Afirka, hakan ya haddasa matsaloli masu da kuma lalata amfanin gona, lamarin da ya shafi mutane kusan miliyan 68.

Farin da ya fara ne tun a farkon shekarar 2024, wanda ya kawo cikas ga amfanin gona da kiwo, sannan kuma ya haifar da karancin abinci da kuma illa ga tattalin arzikin kasashen yankin.

A yayin da ake tunkarar kalubale a yankin kan samar da abinci, shugabannin kasashe 16 na SADC sun gana a Harare babban birnin kasar Zimbabwe.

A cewar sakataren zartaswa na kungiyar ta SADC Elias Magosi, kusan mutane miliyan 68, wato kashi 17% na al’ummar yankin, na bukatar taimako.

Magosi ya ce, “Lokacin damina na 2024 ya kasance mai cike da kalubale, inda akasarin sassan yankin ke fama da munanan fari sakamakon rashin ruwan sama.

Yankin kudancin nahiyar na fuskantar fari mafi muni cikin shekarun baya-bayan nan, sakamakon gaurayen yanayi na El Nino da ake samu, wanda ke faruwa a lokacin da ruwan gabashin tekun Pasifik ya yi zafi matuka,  da kuma sauyin yanayi da ake samua  duniya, da kuma matsakaicin yanayin zafi da ke haifar da hayaki mai gurbata muhalli.

Tuni kasashen Zimbabwe da Zambia da Malawi suka ayyana matsalar yunwa a matsayin bala’I da ke bukatar aikin gaggawa a kasashensu, yayin da Namibiya da Lesotho suka bukaci agajin jin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments