A bayanin da rundunar tsaron sararin samaniyar Iran ta fitar dangane da hare-haren ya kunshi cewa; Tsarin wucin gadi na ‘yan sahayoniya ya kai hare-hare akan cibiyoyin soja a gundumomin Tehran, Khuzistan da kuma Ilam da samfiyar yau.
Cibiyar tsaron sararin samaniyar Iran ya kara da cewa;
“ Muna sanar da al’ummar Iran cewa, tare da cewa jami’an jamhuriyar musulunci ta Iran sun yi gargadi ga ‘yan sahayoniya masu aikata laifi kuma haramtacciyar kasa akan su kaucewa duk wani abu na wuce gona da iri,sai dai kuma da safiyar yau wannan kasar ta bogi, ta yi tsokana. Ta kai hari akan wasu cibiyoyin soja a cikin gundumomin Tehran, Khuzistan da Ilam,amma kuma makaman tsaron sararin samaniyar Iran sun kakkabo makaman da aka kawo hari da su. Harin ya barna kadan, kuma a halin yanzu ana cigaba da gudanar da bincike.
A halin yanzu, muna yin kira ga al’ummar Iran da su kwantar da hankalinsu, su kuma cigaba da bin diddigin labarin abinda yake faruwa ta hanyar kafafen watsa labarun kasa, kar su saurari abinda makiya suke yadawa.”