Rundunar Sojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Wasu Garuruwan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Rundunar sojin Yemen ta kai wani hare-hare kan wasu muhimman wurare a Jaffa da Ashkelon a haramtacciyar kasar Isra’ila Rundunar sojin Yemen ta sanar da

Rundunar sojin Yemen ta kai wani hare-hare kan wasu muhimman wurare a Jaffa da Ashkelon a haramtacciyar kasar Isra’ila

Rundunar sojin Yemen ta sanar da kai farmaki kan wasu wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Jaffa da yankin Ashkelon da suke kudancin Falasdinu da aka mamaye.

Rundunar sojin ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Rundunar sojin ta kai harin ne da jiragen sama marasa matuka ciki, inda ta jaddada cewa, hare-haren sun samu nasarar isa inda aka saita su tare da janyo munanan hasarori ga haramtacciyar kasar Isra’ila.

Sojojin kasar ta Yemen sun tabbatar da cewa: Za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na soji domin mayar da martani kan laifukan da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi a Gaza da Lebanon, kuma wadannan hare-hare ba za su tsaya ba, face an dakatar da matakan wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu musamman a Zirin Gaza, da kuma dakatar da farmakin kan kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments