Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun fitar da bayani akan hare-haren da su ka kai wa sansanoni da cibiyoyin sojan HKI, tare da jaddada cewa matukar ‘yan sahayoniyar ko Amurka su ka mayar da martani, to za su dandana kudarsu.
Bayanin dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; A karkashin manufofin jamhuriyar musulunci ta Iran muna jan kunnen gwamnatin ‘yan ta’adda ta Amurka da cewa, matukar ta yi tarayya wajen kai wa Iran Iran to za su fuskanci mayar da martani mai tsanani. Bugu da kari sanarwar ta ce; Amurka tana da alhaki akan abinda ashararancin da ‘yan sahayoniya masu kashe kananan yara suke yi.
Wani sashe na sanarwar dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kunshi kwantarwa da al’ummar Iran hankali akan cewa; sojojin karar suna cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar makiya da dakile duk wasu manufofinsu.
Harin na dakarun kare juyin musulunci na Iran ya zo ne kwanaki 10 bayan harin da HKI ta kai wa karamin ofishin jakadancin Iran dake birnin Damascuss na kasar Syria, wanda ya yi sanadin shahadar masu bayar da shawara a harkokin soja su 7.
Tabbas rikici ba Abin so bane anma Israeli tana bukatar tarbiya irin ta bakin wuta
Mun gode da sakonka ALlah bar zumunci. bi salam