Search
Close this search box.

Najeriya: Tinubu Ya Ce Ya Cire Tallafin Makamashi Ne Don Hana Tattalin Arzikin Kasar Tsiyacewa

Shugaba Bola Ahmed Tunubu na tarayyar Najeriya, ya bayyana cewa cire tallafin makamashin da yayi a farkon wannan shekarar ya zama dole don kada kasar

Shugaba Bola Ahmed Tunubu na tarayyar Najeriya, ya bayyana cewa cire tallafin makamashin da yayi a farkon wannan shekarar ya zama dole don kada kasar ta tsiyace. Shugaban ya bayyana haka ne a jiya lahadi a taron tattalin arziki ta duniya = wato wold Economic Furum (WEF) da ke  gudana a halin yanzu a birnin Riyad na kasar Saudiya.

Ya kuma kara da cewa bayan cire tallafin gwamnatinsa ta dauki matakai na ganin ta rage radadin cere tallafin kan masu karamin karfi musamman matasa. Duk da cewa tasirin cire tallafin ya shafi mafi yawan mutanen kasar.

-Tsohon gwamnar jihar Jigawa Sule lamido ya ce tafiyan da wasu gwanonin Arewa suka yi zuwa kasar Amurka don halattan taro ko jawabi kan al-amuran tsaro a kasar ya nuna jahilcinsu ga kundin tsarin tarayyar Najeriya.

Kafin haka dai gwamnonin jihohin Arewa sun je kasar Amurka a kwanakin da suka gabata don halattan taron kan harkokin tsaro a arewacin kasar wanda jami’ar harkokin tsaro ta kasar Amurka wato Us Institute of peace (USIP) ta shirya.

Lamido ya kara da cewa al-amuran tsaro kacokam dinsa harkar gwamnatin tarayya ne, jihohi basu ta fada a wannan bangaren.

Ya kamala da cewa da sun je Amurka don neman hanyoyin bunkasa ayyukan noma, kiwon lafiya da kuma matsalolin jihohinsu da hakan yayi dai dai. Amma tafiya da sunan harkokin tsaron kasa jahilci ne ga kundin tsarin mulkin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments