Rahotanni sun bayyana cewa da dubun dubatan alummar kasar birtaniya suka cika manyan titunan birnin London a ranar ta 28 ta gudanar da zanga-zangar yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a gaza tare kuma da nuna goyon bayan alummar falasdinu da ake zalunta,
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zanar da suka fito daga garuruwa daban-daban na birtaniya sun hallar a birnin London ne domin nuna bacin ransu game da ci gaba da kashe mata da yare kanana da Isra’ila ke yi a Gaza,
Babban sakon da masu zanga-zangar suke son aikewa da shi, shi ne neman a gaggauta kawo karshen yakin Gaza da kuma bada dama a aike musu da taimakon agaji , da kuma haramta aikewa Isra’ila makamai .
Wanann yana zuwa ne adaidai lokacin da aka shiga wata na 7 da HKI ke ci gaba da yin kisan kare dangi kan alummar Gaza tare da goyon bayan kawayenta Amurka da birtaniya.