Amurka: Limamai Da Malaman Addini Fiye Da 100 Ne Suka Bayyana Goyon Bayansu Ga Daliban Jami’o’i Masu Goyon Bayan Falasdinawa

Limaman masallatai a kasar Amurka da kuma malaman addini fiye da 100 ne suka bayyana goyon bayansu ga daliban jami’o’ii a kasar wadanda suke zanga

Limaman masallatai a kasar Amurka da kuma malaman addini fiye da 100 ne suka bayyana goyon bayansu ga daliban jami’o’ii a kasar wadanda suke zanga zangar goyon bayan falasdinawa, wadanda sosjojin HKI suke  kashewa a gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya bayyana cewa, daliban Jami’ar Colombia  na birnin NewYork ne suka fara zaman dirshen a farfajiyar Jami’ar a farkon wannan watan, inda suke bukatar a kawo karshen yaki a gaza sannan a kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci daga kogi zuwa teku.

Tun makon da ya gabata ne shuwagababbin Makarantu da dama a kasar ta Amurka su ke kiran yansanda don murkushe dalibai masu zanga zanga goyon bayan Falasdinawa a makarantunsu.

A ranar jumma’a ce limamai da malamai kimani 135 a Amurka bada sanarwan nuna goyon bayan su ga daliban Jami’o’ii a kasar masu goyon bayan Falasdinawa a gaza.

Limaman sun yi addu’a ga daliban da kuma fatan zasu sami nasarar tursasawa gwamnatin kasar Amurka ta canza ra’ayinta dangane yakin da ke faruwa a kasar Falasdinu a musamman a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments