Kungiyar mata ta kwallon kafar ta Iran ta sami nasarori har sau uku, ta kuma yi canjaras sau daya da a karshe hakan ya mayar da ita zama gwarzuwa a wasannin Asiya ta Tsakiya.
Ita dai kungiyarn kwallon kafan ta mata ta Iran da shekarunsu ke kasa da 18 ta sami galaba akan twakwararta ta kasar Kyrkizia ne a watan da aka yi a jiya Lahadi.
Gabanin wannan kungiyar ta sami nasara akan Ubakestan da ci 4-2, sai kuma da Turkimanistan da ta zurwa kwallaye 7, yayin da ta ci kungiyar kwallon kafa ta Tajiksitan kwallaye 5.