Rundunar IRGC Ta Bayyana Cewa Amurka Ta Sake Dawo Da Yaki Kan Iran Duk Tare Da Gargadinta

Amurka ta sake tada yaki a kudancin kasar Iran a safiyar yau Lahadi duk tare da gargadin dakarun IRGC bangaren ruwa, wanda ya zo bayan

Amurka ta sake tada yaki a kudancin kasar Iran a safiyar yau Lahadi duk tare da gargadin dakarun IRGC bangaren ruwa, wanda ya zo bayan da kasar Iran ta rufe mashigar ruwa ta Hurmuz saboda hare hare na farko.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar CENTCOM na kasar Amurka a kasashen Asia na cewa sun kai hare hare kan wasu wurare a kudancin kasar Iran tare da umurnin shugaba Trump da nufin rage karfin Iran na kula da mashigar ruwa ta Hurmuz.

Kafin wannan sanarwan ta CENTCOM mutane a garuruwan Asaluyeh da Bandar Dayyer na lardin Busher sun bada labarin jin karar fashewar makamai a wurare da dama a yankin, kamar yanda Farnews ya bada labara.

Daga bayan kamfanin dillancin labaran IRIB na gwamnatin kasar Iran ya tabbatar da aukuwar hare hare a Bandar Abba da wasu wurare uku wadanda suka hada da birnin Sirik a lardin Hurmuzghan. Har’ila yau sun kai hare hare kan garin Minab da Jask. Sannan daga kudu kuma kai hare hare kan Chabahar da tsibirin  Konarak.

Sai kuma a lardin Khuszistan sun kai hare hare kan Hendijan, Mahshahr da Abadan. Kungiyoyin bada agaji sun je wadan nan wurare. Sannan IRGC ta bada sanarwan rufe mashigar ruwa ta Hurmuz har zuwa lokacinda Amurka zata kawo karshen wadan nan hare hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted