Ribadu Ya Gana da Sakataren Yakin Amurka Kan Batun Kashe Kiristoci A Nijeriya

Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta

Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya.

Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki da gaggawa da Nijeriya wajen rage hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke kara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da kungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a kauyuka, da coci-coci da gonaki. Ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ruwaito karuwar kashe-kashe, inda alkalumman baya-bayan nan ke nuna cewa sama da Kiristoci 7,000 aka kashe cikin watanni bakwai na 2025. Taron ya biyo bayan sace dalibai 215 da malamai 12 daga wata makarantar Katolika a jihar Neja, wanda ya kara tayar da hankalin jama’a kan tabarbarewar tsaro. Wannan lamari ya kuma kara sa Amurka cikin damuwa kan karuwar ayyukan sace mutane da kashe-kashe a kauyuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments