Kafamin dillancin labarun “Reuters ya nakalto cewa; harin da sojojin kasar Yemen su ka kai a kamfanin Aramco na man fetur din Saudiyya dake Zahran a gabashin kasar, ya yi barna mai yawa.
Labarin ya kuma ce harin na jiya Talata ya yi barna mai yawa ta yadda gobra ta tashi a cikin babban ginin kamfanin sannan kuma ta ci gaba da lakume dogayen gine-gine.
Da marece jiya Laraba ne dai sojojin gwmanatin Sanaa su ka sanar da kai harin daukar fansa akan kamfanin “Aramco na Saudiyya dake Zahran a gabashin kasar. Haka nan sun sanar da kai wasu harin akan filin saukar jiragen saman a Sarki Khalid a birnin Riyadh da shi ma gobara ta tashi a cikinsa.
Kwanaki hudu a jere kenan sojojin na Yemen suna kai wa filin saukar jiragen saman a Riyadh hare-hare, da hakan ya dakatar da aiki a cikinsa.
Sanarwar da sojojin na Yemen su ka yi, ta kunshi bayyana cewa sun yi amfani da makamai masu linzami ne samfurin ” Ballistic” wajen kai hare-haren, kuma sun isa inda aka harba su.
Bugu da kari sanarwar sojojin na Yemen ta yi kira ga dukkanin masu zama a kusa da kamfanonin man Saudiyya da su yin isa da su, domin za su fuskanci kai hare-hare.
Da safiyar yau Laraba ne dai ma’aikatar makamashi ta Saudiyya ta sanar da cewa; gobara ta tashi a cikin kamfanin na Aramco dake Zahran, a gabashin kasar, amma babu wanda ya jikkata.