Wakilin shugaban kasan Iran na musamman kan al-amuran kasar Afghanistan ya bayyana cewa, dole ne kasashen yankin Asia su dauki matakan da suka dace don warware matsalolin tsaro da zamantakewa na kasar Afghanistan saboda halin da kasar take ciki barazana ce ga al-amuran tsaro a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Hassan Kazemi-Qumi yana fadar haka a taro na biyu dangane da kasar Afganistan a nan Tehran.
Qumi ya kara da cewa halin da mutanen kasar Afgansitann a Tehran bai da kyau so sai, kuma matsalolin suna da dangantaka da mamayar da kasar Amurka ta yi wa a kasar na tsawo shekaru 20.
Labarin ya kara da cewa wakilai na musamman na kasashen Iran, Pakistan, China da kuma Rasha ne suka hadu a taron.
Kasashen 4 sun bayyana bukatar kasashen yankin su yunkura don ganin kasar Afganistan da mutanen kasar sun fita daga mummunan halin da suke ciki na rashin tsaro da kuma yaduwar ayyukan ta’addanci a kasar da kuma yankin.
Taron ya bayyana cewa dole ne a kula da kan iyakokin kasar Afganistan kamar yadda ya dace, sannan a yi maganar komawa gida na yan gudun hijirerar kasar wadanda suke samun mafaka a kasashe makota, wadanda kuma suka kai kimani kasha 30 na yawan mutanen kasar. Banda haka akwai bukatar a kaiwa mutanen kasar agajin gaggawa don irin mummunar halin da suke ciki, tare da gahin kai da gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa kasar Iran kadai tana daukar bakwancin mutanen kasar Afganistan kikanmi miliyon 6. Daga karshen taron ya bayyana cewa gabatar da wadannan shawarori ba shihsigine a cikin al-amuran kasar ba.