Rasha Ta Yi Luguden Wuta Kan Cibiyoyin Makamashin Kasar Ukraine

Gwamnatin Rasha ta kai hare-hare da makamai masu linzami da ya girgiza babban birnin kasar Ukraine da wasu garuruwa na daban Wadannan hare-hare da kasar

Gwamnatin Rasha ta kai hare-hare da makamai masu linzami da ya girgiza babban birnin kasar Ukraine da wasu garuruwa na daban

Wadannan hare-hare da kasar Rasha ta kai kan kasar Ukraine sun hada da makamai masu linzami wanda shi ne mafi girma a cikin kusan watanni uku, inda hare-haren suka hada da harba makamai masu linzami 120 da jiragen sama marasa matuka ciki 90, da suka janyo mutuwar mutane akalla goma tare da raunata kimanin wasu 20 na daban a sassa daban-daban na kasar, baya ga mummunar illa ga tsarin makamashin kasar ta Ukraine.

Rundunar sojin saman Ukraine ta sanar da cewa: Hare-haren da Rasha kai kan kasarta yana matsayin wani daren jahannama ne, duk da jami’an tsaron sararin samaniyyar kasar sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da sukakai 144.

A nata bangaren, ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hare-haren kan dukkanin wuraren da ake samar da kayayyakin makamashi da suke tallafawa rukunin masana’antu na sojan Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments