wakilin dindin din na kasar rasha a kungiyoyin kasa da kasa a viyanna mika’il Ulyanov yayi gargadin cewa duk wani hari da za’a kai kan cibiyoyin nukiliya zai kasance babban laifi kuma ya sabama dokokin kasa da kasa,
haka zalika ya wallafa a shafinsa na X cewa duk wani hari da zaa’a kai cibiyoyin nukiliya babban laifi ne , don haka kai harin kan cibiyar nukiliya ta bushahr zai zama wani babban bala’I ga kasashen tekun fasha,don haka ya zama wajibi a dakatar da daukar wannan matakin,
wadannan bayanai suna zuwa ne bayan jita-jitar da ake yadawa na cew an kai hari kan wani sashi na cibiyar nukiliyar bushahr.
hukumar kula da makamashin nukiliyar kasar iran ta mayar da martani inda ta musanta jita-jitar kuma ta ce cibiyar nukiliya ta bushahar tana nan lafiya lau ba a bin da ya shafeta
haka zalika ta kara da cewa cibiyar nukiliya ta bushahar tana nan lafiya lau,kuma a yanayin da ya dace kuma kowanne bangare yana gudanar da ayyukansa ba tare da tsayawa ba,