Rasha Ta Musanta Labari Mai Cewa Ta Na Samun Taimakon Makamai Masu Linzami Daga Kasar Iran

Fadar Kremlin ta musanta rahoton mai cewa kasar Rasha tana samun tallafin makamai masu linzami masu cin karamin zango daga kasar Iran. Tashar talabijin ta

Fadar Kremlin ta musanta rahoton mai cewa kasar Rasha tana samun tallafin makamai masu linzami masu cin karamin zango daga kasar Iran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa:

Iran kawar kasar Rasha ce a cikin al-amura da dama, wadanda suka hada da kasuwanci da sauransu. Kuma kasashen biyu suna tattaunawa a kan al-amura da dama da ke tsakaninsu.

Ya ce rahotannin da kafafen yada labaran kasashen yamma suke yadawa a kan wannan batun ba duka ne gaskiya ba.

Kafin haka dai jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka, a ranar 6 ga watan Satumba ta rubuta rahoto na musamman wanda ta samu daga majiyoyin Amurka da Turai wadanda ba’a fayyacesu ba, kan cewa Iran ta tura makamai masu linzami zuwa kasar Rasha don taimaka mata a yankin da take fafatwa a kasar Ukraine.

Tashar talabijin ta CNN ta maimata abu guda, haka ma kungiyar tarayyar Turai ta sake yin wannan zargin. Sai dai gwamnatin kasar Iran ta musanta wannan rahoton.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments