Rasha Ta Kakkabo Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Na Ukraine 38 A Kwana Daya

Gwamnatin Rasha ta sanar da kakkabo jiragen saman yaki marasa matuka ciki na kasar Ukraine guda 38 a kusa da kan iyakar kasarta Majiyar tsaron

Gwamnatin Rasha ta sanar da kakkabo jiragen saman yaki marasa matuka ciki na kasar Ukraine guda 38 a kusa da kan iyakar kasarta

Majiyar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa: Akalla mutane hudu ne suka mutu a wani luguden wuta da sojojin kasar Ukraine suka yi kan yankin Belgorod na kasar Rasha da ke kusa da kan iyaka da Ukraine, sannan sojojin Rasha sun yi nasarar kakkabo jiragen saman yaki marasa matuka ciki mallakin Ukraine guda 38 a yankunan da suke kusa da kan iyaka da Rasha. Wadannan manyan hare-haren, Ukraine ta yi nufin kai su ne domin daukan fansa bayan kwana daya da fuskantar harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan kasar ta Ukraine a ranar Litinin da ya gabata.

Jami’an Rasha sun watsa rahoton fuskantar hare-hare a wasu wurare a shiyar yammacin kasar daga Ukraine. Yayin da ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa: Sun harbo jiragen Ukraine marasa matuka ciki guda 38 ne a cikin dare a yankunan da suke kusa da kan iyakar kasashen biyu. Ma’aikatar ta kara da cewa: Na’urorin tsaron sararin samaniyar Rasha sun kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki guda uku ne a yankin Belgorod, yayin da jirage marasa matuka ciki guda 7 aka harbo su a yankin Kursk, biyu kuma a yankin Voronezh, gami da jiragen sama yakin Ukraine guda 21 a sararin masaniyar Rostov, da kuma guda 5 a yankin Astrakhan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments