Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta fada a jiya Laraba cewa; Abinda muke zato daga hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa shi ne ta kasance ‘yar ba-ruwanmu a cikin batun da ya shafi siyasa.
Zakharova ta kara da cewa; Akan Iran abinda mu ka tsammata daga hukumar ta makamashin Nukiliya ta kasa da kasa shi ne ta nuna halayyar ‘yar-ba ruwanmu.
Jami’ar diplomasiyyar ta Rasha ta kuma ce; Kungiyoyin kasa da kasa suna da masaniya akan cewa; kasashen yamma ne su ka kawo cikas a cikin yarjeniyar Nukiliyar Iran,amma Tehran a kodayaushe tana nuna cewa a shirye take ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta.
A wata hira da shugaban hukumar ta Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya yi da kamfanin dillancin labarun Italiya ( ANSA) ya riya cewa Iran ta tara tataccen Uranium da za ta iya sarrafa shi a fagen aikin aikin soja.
Iran din dai ta yi watsi da wannan batu na Grossy,inda shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami ya ce; ba zai zama karbabbe ba a ce hukumar makamashin ta Nukiliya tana tuhumar Iran,alhali tana kau da kai daga daya bangaren.