Shugaban kasar Rasha viladmir putin da na Amurka Donald Trump sun yi watsi da bukatar da kasashen turai suka gabatar na wucin gadi kan batun tsagaita bude wuta, sun bukaci gwamnatin Kiev ta dauki matakin gaggawa don kawo karshen rikicin.
Mai kula da siyasar wajen na fadar Kremlin Yuri Ushakov ya bayyana a wata tattaunawa ta wayar tarho ta tsawon awa daya da rabi dukkan shuwagabannin sun cimma matsaya cewa tsagaita wuta na wucin gadi zai kara tsawaita rikicin ne kawai,
Kafin zaman da trump yayi da shugaban kasar Ukrain zelenskiy ya fadi cewa akwai kyakkyawar dama da suke da ita da zaa cimma matsaya, kuma ya bayyana ta a matsayin wadda za ta amfani kasar ukrain da sauran bangarorin,
Kasar rasha dake da iko da kasha 90% da yankin Donbas tana so Ukrain ta janye sojojinta daga wajen da take da iko dashi kasha 10%, domin rasha na da iko da kashe 5 cikin 100 ne Ukrain.