Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa kallon da kasar Iran take yi wa kasashen Afrika kallon abokan tarayyar ne da kuma girmamawa.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a taro na 2 tsakanin JMI da kasashen Afrika wanda aka gudanar a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa kasar Iran a shirye take ta daga matsayin huldar kasuwanci da tattalin arziki da kasashen Afrika.
A jiya jumma’a 26 ga watan Afrilu ne aka gudanar da taro karo na 2 tsakanin kasashen Afrika da JMI inda wakilan kasashe Afirka kama daga shuwagabannin gwamnatoci, ministocin harkokin kasuwanci, da manya- manyan jami’an gwamnati na kasashen Afirka fiye da 30 suka sami halattar taron.
mataimakin shugaban kasar Zimbawe Constantino Chiunga wanda da shi da tawagrsa suka wakilci kasar a taron, ya fada wa shugaba Ra’isi cewa akwai bukatar kasashen biyu su kara fadada dangantakar da ke tsakaninsu fiye da yadda take a halin yanzu.