Ra’isi:  Idan ‘Yan  Sahayoniya Da Masu Kare Su Su Ka Tafka Kuskure, Za Su Fuskanci Mayar Da Martani Na Hakika Daga Iran

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi wanda ya gana da mataimakin shugaban majalisar koli ta ‘yan shi’ar kasar Lebanon, Sheikh Ali Khatib, ya bayyana cewa;

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi wanda ya gana da mataimakin shugaban majalisar koli ta ‘yan shi’ar kasar Lebanon, Sheikh Ali Khatib, ya bayyana cewa; Harin da ‘yan sahayoniya su ka kai wa karamin ofishin jakadancin Iran a Syria ya ci kasa, kuma harin da Iran ta kai na gargadi ne kawai.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa, Idan har ‘yan sahayoniya da masu kare su, su ka tafka kuskuren sake kai wa manufofin Iran hari, to za su fahimci hakikanin mayar da martani daga Iran.

Shugaban na kasar Iran ya kuma ce, jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta yi imani da cewa batun sulhun da ake Magana a kansa a tsakanin Falasdinawa da ‘yan sahayoniya zai haifar da Da,mai ido ba, hanya daya ta kwato da hakkoki ita ce gwagwarmaya.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments