Rahoto: Dakarun Yemen Sun Gagari Gwamnatin Isra’ila

Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana

Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen

Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana a cikin wani rahoto na baya-bayan nan cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fama da babbar matsala ta soji da tsaro, bayan da ta kasa dakatar da hare-haren da Yemen ke kai mata hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki tun daga ranar 19 ga Oktoban shekara ta 2023.

Jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila sun bayyana bangaren Yemen a matsayin “wanda ya fi kowa hauka a yankin,” suna masu gargadin cewa shiga fafatawar da suke yi da su zai haifar da mummunan sakamako ga haramtacciyar kasar Isra’ila, ganin yadda suke ganin dakarun Yemen ba za su ja da baya ba.

Jaridar ta yi nuni da cewa: Jami’an leken asirin mamayar Isra’ila sun fara ayyukan kai hare-hare kan kasar Yemen a cikin lokacin bazarar shekara ta 2024 a kokarinsu na kawo cikas ga dakarun Yemen, amma har ya zuwa yanzu ba su yi nasara ba wajen rage tasirin hare-haren da ake kaiwa kan muhimman yankunan haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments