Wani rahoto ya bayyana irin goyon bayan da Birtaniyya ke baiwa kungiyoyi masu dauke da makamai a Siriya
Wani rahoto mai taken “Lokacin da Biritaniya ta Taimakawa Al-Qaeda a Siriya” ya bayyana cewa: Birtaniya tana goyon bayan kungiyoyi masu dauke da makamai a Siriya ta bayan fage, tun a shekara ta 2011 don hambarar da tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, tare da hadin gwiwar Amurka da gwamnatocin kasashen Larabawa da na musulmi.
Rahoton, wanda marubuci Mark Curtis ya wallafa a shafin yanar gizon Birtaniya na “declassifieduk”, ya bayyana matakai Goma na Wuta da Siriya da kasashen yankin suka fuskanta, wanda ya fara da shiga tsakani na kasa da kasa, inda Amurka da Birtaniya suka goyi bayan abin da ake kira ‘yan adawar Siriya”. Ta hanyar wadata su da kudade da karfin soji tare da hadin gwiwar kasashen Larabawa.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan gangamin a asirce, ita ce kungiyar Jubhatu-Al-Nusra masu kafirta musulmi, wacce reshe ce ta kungiyar ta’addanci ta Al-Qaeda a kasar Siriya, wadda Abu Muhammad al-Julani ya kafa, wanda daga bisani ya kira dakarunsa masu dauke da makamai da “Hay’at Tahrir al-Sham.” A bangaren kudi kuwa, an kiyasta taimakon da Amurka ke baiwa kungiyoyin da suke dauke da makamai da cewa ya kai dala biliyan daya a lokacin, yayin da kasashen Larabawa suka ba da karin biliyoyin kudade.