Rahoto: Isra’ila tana kai wa ‘yan jarida hari ne da gangan a Gaza don boye laifukanta

A cikin wani rahoto na jaridar New York Times, ‘yar jarida Lydia Polgreen ta bayar da hujjar cewa “Isra’ila” tana kai hari ga ‘yan jarida

A cikin wani rahoto na jaridar New York Times, ‘yar jarida Lydia Polgreen ta bayar da hujjar cewa “Isra’ila” tana kai hari ga ‘yan jarida a Gaza da gangan don kawar da hujjoji kan laifukan yaki da take tafkawa a yankin.

Polgreen ta ba da misali da kisan da aka yi wa dan jarida Anas al-Sharif a wani harin da Isra’ila ta kai a farkon wannan watan a matsayin shaida na kai hari kan ‘yancin ‘yan jarida.

Sojojin Isra’ila sun yi ikirari ba tare da gabatar da kwararan hujjoji ba, cewa al-Sharif kwamandan Hamas ne da ke aiki a karkashin inuwar dan jarida.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da suka hada da kwamitin kare ‘yan jarida na kasa da kasa, duk sun yi tir da harin tare da bayyana shi a matsayin laifin yaki. Akalla ‘yan jarida 192 ne aka kashe a Gaza tun lokacin da aka fara yakin, adadin da ba a taba ganin irinsa ba idan aka kwatanta da sauran tashe-tashen hankula da aka yi fama da su a wasu wurare a duniya.

Polgreen ta lura cewa “Isra’ila” ta hana ‘yan jaridu na kasa da kasa shiga Gaza, wanda ya bar ‘yan jaridu na cikin gida a matsayin shaida na farko kuma wadanda su ne kawai za a iya jin wani wani rahoto daga gare su kan abin da ke faruwa a Gaza.

Marubuciyar ta kuma soki martanin da kasashen duniya suka yi, tare da bayyana shi a matsayin abin kunya da takaici. Sannan ta yi gargadin cewa idan ba a shawo kan kashe-kashen da ake yi wa ‘yan jarida a Gaza ba, nan ba da jimawa ba za a rasa  wanda zai bayar da bayan ikan halin da ake ciki da kuma barnar da Isra’ila ke yi a cikin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments