Qalibaf: Zaben shugaban kasar Amurka ba shi da wani tasiri a kan manufofin Iran

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana irin karfin da kasar ke da shi na cimma muradunta, yana mai jaddada cewa zabukan da za a

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana irin karfin da kasar ke da shi na cimma muradunta, yana mai jaddada cewa zabukan da za a gudanar a Amurka ba zai iya yin wani tasiria  akan Iran ba.

Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi a matsayin martani ga zaben shugaban kasa da aka gudanar a Amurka.

Kakakin ya kara da cewa, yadda Iran take aiki da karfi da kuma taka tsantsan bisa tsarin juyin juya halin Musulunci, shi ne ke sanya makiya suna shakkun yin wani shishigi a kan lamarin kasar.

Kasancewar Iran kasa mai ‘yanci yayin daukar matakai da kuma hana duk wani dogaro ga kasashen waje, wannan wani tushe ne na tsarin Jamhuriyar Musulunci, inda ya kara da cewa an samu dukkanin nasarori a cikin wannan tsari a kasar.

Kasashe masu tasowa kamar Iran, wadanda babu wanda zai iya mallake su, sun dogara da karfinsu na cikin gida, kuma za su kara taka rawar gani a tsarin duniya a nan gaba, in ji shi.

A jawabin nasa, Qalibaf ya ce hanya mafi dacewa ta dakile duk wani matsin lamba da barazana ita ce magance matsalolin cikin gida, musamman matsalolin tattalin arziki.

A yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a Amurka, an zabi Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 47, wanda Iran ke kallon cewa ba zai yi wani tasiri a kan manufofinta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments