Prime ministan kasar sudan Kamil idris yayi gargadin cewa aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen waje a kasar Sudan zai kara ruruta wutar rikicin ne da kuma keta yancin kasar, kuma kalaman nasa suna cewa ne bayan rahoton da aka fitar game da cin zarafin dan Adam da aka yi a El-fasher dake arewacin Darfur.
Sudan ta dade tana cikin rikci wanda ya haddasa yunkurin juyin mulki sau 20 a kasar da kuma yakin basasa guda biyu, lamarin ya kara taazzara ne bayan rikicin da ya barke a baya bayan nan, wanda ke barazanar ga zaman lafiya yankin , sai dai har yanzu kasashen duniya basu cimma matsaya ba kan yadda zaa samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ba.
Abin da ya faru a baya bayan nan sojojin kungiyar Rsf sun kai mummunan hari a El-fasher , inda majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka zarge su da yin kisan gilla, yanke hukumci kisa a filin daga da cin zarafin yan gudun hijira duk da yake cewa kungiyar ta Rsf ta karyata zargin.
Daga karshe Idris ya bukaci majalisar dinkin duniya ta bayyana kungiyar Rsf a matsayin kungiyar yan taadda, kuma yayi watsi da ra’ayin aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a kasar don kasancewarsu zai kara ruruta wutar rikici ne kawai.