Pezeshkian: Umarnin Kisan Sayyid Nasrallah Ya Zo ne Daga New York

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasashen duniya ba za su manta da cewa an ba da umarnin harin ta’addancin Isra’ila na kashe babban

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasashen duniya ba za su manta da cewa an ba da umarnin harin ta’addancin Isra’ila na kashe babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta Lebanon Sayyed Hassan Nasrallah daga birnin New York.

An dai kai hare-haren ne a daidai lokacin da firaministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ke gabatar da jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York.

A cikin sakon ta’aziyya da ya aike  da shi, Pezeshkian ya ce Amurka ba za ta iya wanke kanta daga hada baki da yahudawan sahyuniya a harin ta’addancin da aka kaiwa shugaban kungiyar Hizbullah ba.

Ya kara da cewa harin ta’addancin da Isra’ila ta kai a ranar Juma’a a yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon da kuma shahadar fitattun masu fafutuka na gwagwarmaya, musamman Nasrallah, zai kara karfafa “bishiyar tsayin daka.”

Shugaban na Iran ya yi nuni da cewa, shugaban kungiyar Hizbullah abin alfahari ne ga musulmi, kuma a karshe ya cimma burinsa na tsawon lokaci wato samu shahada a tafarkin gaskiya.

Pezeshkian ya ce kalmomi ba za su iya bayyana bajintarsa ​​da ci gaba da kokarinsa na yakar makiya ba, ya kuma kara da cewa Hizbullah za ta kara haskakawa bayan kisan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments