Pezeshkian: Martanin Iran Zai Yi Daidai Da Sabon Halin Da Ake Ciki Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Martanin Iran zai yi daidai da sabon halin da ake ciki idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Martanin Iran zai yi daidai da sabon halin da ake ciki idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan kasarsa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Bolivia Luis Arce Catacora a birnin New York na kasar Amurka, ya jaddada cewa Iran za ta daidaita ayyukanta daidai da duk wani sauyi na al’amuran kasa da kasa idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan Kasarsa.

Pezeshkian ya bayyana cewa, manufofin bai-daya na Amurka suna yin illa ba wai ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kadai ba, har ma da dukkan kasashen da ba su dace da alkiblarta ba. Ya kuma jaddada bukatar kasashe masu cin gashin kansu su kara karfinsu na kimiyya da na musamman don kare muradunsu da diyaucin kasa.

Ya yi nuni da cewa, makomar huldar dake tsakanin Iran da Bolivia ta dogara ne da ra’ayi daya da kuma kudurin manyan jami’an kasashen biyu. Ya jaddada cewa Iran ta mallaki wannan tsayayyen kuduri, kuma manufofi da hanyoyin jami’an Bolivia za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance yanayin hadin gwiwa a nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments