Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana sakon kasarsa da cewa na yada zaman lafiya da kyautata dangantaka da dukkanin kasashe musamman ma makwabta.
Pezeshkian wanda ya isa Kazan bisa gayyatar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin domin halartar taron koli na kasashen BRICS karo na 16, inda ya bayyana hakan a wani bangare na farko na ziyarar tasa a kasar Rasha da kuma ganawarsa da firaministan kasar Indiya Narendra Modi.
Shugaba Pezeshkian ya ce “Ina fatan kasashen da ke da’awar kare hakkin bil’adama za su taimaka wajen dakile laifuka da kashe-kashen da gwamnatin yahudawan sahyuniya ke aikatawa, ta hanyar sauya salonsu da kuma dakatar da goyon bayan da suke ba wa wannan gwamnati ta Sahayoniya.”
Shugaban na Iran ya kara da cewa: “Mun yi imanin cewa yaki yana kawo cikas ga ci gaban kasashe, a saboda haka muke yin tsayin daka don hana yaduwar rikici da tashin hankali a yankin, amma gwamnatin yahudawan sahyoniya ta nuna a fili kan cewa tana neman yaki ne kawai ba zaman lafiya ba.”
Shugaba Pezeshkian ya yi nuni da cewa, abin bakin cikin shi ne cewa, a daidai rana ta farko ta kama aikinsa a matsayin shugaban kasa a hukumance, gwamnatin Sahayoniya ta yi kokarin kawo cikas ga cimma wadannan manufofin ta hanyar kashe Ismail Haniyah a matsayin babban bako na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.