Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce harin makami mai linzami da kasar ta kai kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a baya-bayan nan da nufin dakatar da laifukan gwamnatin yahudawan ne kan laifukan yakin da take aikatawa kan al’ummar yankin, da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin baki daya.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan kasar Netherlands Dick Schoof a wannan Lahadi, bayan da Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami kan sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da kuma sansanonin soji da na leken asiri a duk yankunan Falastinawa da ke karkashin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Wannan farmakin ya zo ne a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da gwamnatin kasar ta yi wa Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, Sayyed Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon, da Birgediya Janar Abbas Nilforushan, mataimakin kwamandan ayyuka na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).
Pezeshkian ya ce Iran ta kai harin makamai masu linzami ne da nufin dakile zaluncin Isra’ila, da dakatar da kokarin yada rikici a yankin da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa farmakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya gudana bisa tsarin dokokin kasa da kasa kuma an kai hari ne kawai kan kaddarori da wurare na soji ba a kan fararen hula ba.
Ya kara da cewa Iran ta kauracewa mayar da martani cikin gaggawa kan laifin ta’addancin da Isra’ila ta aikata na kisan Haniyyah a Tehran da kuma keta hurumin kasarta, bisa fatan ganin cewa yunkurin diflomasiyya zai kai ga tsagaita bude wuta a zirin Gaza.