Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya sake taya zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian murnar lashe zaben shugaban kasar Iran da ya yi a baya-bayan nan, tare da jadda matsayar Saudiyya na kara habbaka ayyukan hadin gwiwa tsakaninta da Iran.
Mohammed bin Salman ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ta gudana tsakaninsa da zababben shugaban kasar Iran Masud Pezeshkian a jiya Laraba, kamar yadda wata sanarwa da kafar yada labaran Saudiyya ta fitar.
Pezeshkian ya bayyana godiya ga bin Salman bisa irin wannan mahanga tasa.
Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun yaba da ci gaban dangantakar Iran da Saudiyya ta samu a matakai daban-daban.
Yarima mai jiran gado ya aike da sakon taya murna ga Pezeshkian bayan nasarar da ya samu a zaben fshugaban kasa zagaye na biyu wanda aka gudanar a ranar 5 ga watan Yuli.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya ce yana da sha’awar bunkasa dangantakar da za ta hada kan kasashen biyu na Iran da Saudiyya, domin cimma buri wanda ya hada bukatunsu na bai daya.
Kasashen Iran da Saudiyya sun dawo da huldarsu shekaru 7 da suka gabata karkashin wata yarjejeniyar da kasar Sin ta jagoranta a shekarar 2023, wadda ta sa bangarorin biyu suka sake bude ofishin jakadancinsu.
Har ila yau Tehran da Riyadh sun amince da aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da aka kulla a watan Afrilun 2001 da kuma wata yarjejeniya da aka cimma a watan Mayun 1998 don bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki, kasuwanci, zuba jari, fasaha, kimiyya, al’adu, wasanni, da harkokin matasa.