Pezeshiyan: Babu Amfanin Tattaunawa Idan An Maida Takunkuman Tattalin Arziki A Kan Iran

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattaunawa da kuma diblomasiyya basa da amfani idan har kasashen E3 sun maida takunkuman tattalin arziki a

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattaunawa da kuma diblomasiyya basa da amfani idan har kasashen E3 sun maida takunkuman tattalin arziki a kan kasarsa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Swiss  Karin Keller-Sutter a gefen taron babban zauren MDD karo na 80.

Ya ce mata ‘muna maraba da tattaunawa ko diblomasiyya amma idan kasashe E3 suka maida takunkuman MDD a kan kasar mu tattaunawa da diblomasiyya basu da amfani a wajemmu’.

Wadannan kasashen turai 3 ko traiko dai sun tada baton maido da takunkuman tattalin arziki na MDD ne a cikin watan Augustan da ya gabata, bayan sun ga Amurka da HKI sun kasa lalata cibiyoyin nukliyar kasar Iran a yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar a cikin watan yuni na wannan shekarar.

Shirin maido da takunkuman dai sun zo a cikin yarjeniyar ta JCPOA ta shekara ta 2015 inda aka ambaci cewa idan kasashen da suka rattabawa yarjeniyar hannu sun ga cewa Iran bata aiwatar da yarjeniyar jcpoa kamar yadda ta dace ba suna da damar maidoda  takunkuman MDD a kan kasar.

Don haka ahalin yanzu sun dauko wannan damar a matsayin makami a kan kasar Iran. Bayan sun kasa cimma nasara a kanta a yakin watan yuli. Don manufar yakin watan yuniitace kifar da JMI da kuma sauya gwamnatin kasar kwatakwata. Daga nan kuma sais u yi da kasar Iran kamar yadda suka yi da kasar Siriya. Su lalata dukkan makamanta su kuma kawokarshen dukkan ci gaban da takesamu ko ta samu na tsawon shekaru kimani 50 da sukagabata. Amma sun kasa yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted