Paparoma Francis ya yi Allah wadai da abin da Isra’ila ke yi a Gaza ta bayyana shi a matsayin abin kunya

Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da kisan kare dangi na “Isra’ila” a zirin Gaza, yana mai bayyana matsalar jin kai a yankin a matsayin

Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da kisan kare dangi na “Isra’ila” a zirin Gaza, yana mai bayyana matsalar jin kai a yankin a matsayin “mai matukar muni kuma abin kunya.

A cikin jawabinsa, Paparoman yayi Allah wadai da harin bama-bamai da aka kai kan fararen hula, inda ya yi ishara da irin mawuyacin halin da ake ciki a Gaza, babu wutar lantarki, ga sanyin hunturu wanda yake janyo asarar rayuka.

Ya ce  ba za mu amince da harin bama-bamai a kan fararen hula ba. “Ba za mu yarda yara suna daskarewa har su mutu ba saboda tsananin sanyi da rashin asibitoci da kayan kiwon lafiya ba.

Fafaroma ya ce, “Buri na a shekara ta 2025 shi ne daukacin al’ummar duniya su rayu cikin aminci a ko’ina, sannan kuma a kawo karshen rikicin da ake fama da shi a duniya, yana mai yin ishara da rikice-rikice a kasashen Ukraine, Sudan, Mozambique, Myanmar, da sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments