Rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da shahadar mayakanta biyu a yammacin kogin Jordan sanadiyyar harin da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai.
Daya daga cikin shahidan shi ne Yusuf Ali Asa-Asa, dan shekaru 37, da kuma Mahmud Abdullah dan shekaru 26, sun kuma yi shahadar ne a jiya Alhamis.
Sanarwar ta kuma ce,an yi batakashi a tsakanin shahidan biyu da kuma ‘yan mamaya gabanin su kwanta dama a unguwar Abu Dhahir dake Jenin a yammacin Kogin Jordan.
Wasu rahotanni daga yankin da lamarin ya faru sun ce, sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa cikin unguwar tare da shiga cikin wani gidan sannan kuma su ka kama wani saurayi Bapalasdine daya. Gabanin su yi awon gaba da shi su jikkata shi ta hanyar dukansa.
Daga lokacin da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta shelanta yaki akan Gaza, take kuma kai wa yankin yammacin Kogin Jordan dake karkashin gwamnatin kwarya-kwaryar Palasdinu hare-hare. A lokaci daya kuma yahudawa ‘yan share wuri zauna suna kai wa gonaki da dukiyar Falasdinawa hare-hare da kona su, da kuma kashe Falasdinawa.