Kasar Pakistan ta ce ba zatayi watsi da da shirinta na nukiliya ba sakamakon barazanar Amurka.
Ministan tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya yi watsi da barazanar da Amurka ta yi a baya-bayan nan kan shirin makamai masu linzami na Pakistan, yana mai jaddada cewa Islamabad ba za ta yi kasa a gwiwa ba kan dabarun tsaronta.
Da yake mayar da martani ga matakin Washington na baya-bayan nan, Ministan Tsaron Pakistan ya bayyana cewa Islamabad ba za ta rage kokarinta na bunkasa makamai masu linzami ba, yana mai jaddada muhimmancin kiyaye karfin tsaron kasar.
“Shirye-shiryen makami mai linzami na Pakistan ba za a iya tattaunawa kansu ba, in ji shi.
Ya kara da cewa, ci gaban da ake samu a duniya, musamman ayyukan da Isra’ila ke yi kan Iran, Siriya, Falasdinu, da Lebanon, na bukatar ci gaba da inganta tsarin tsaron Pakistan don daidaitawa da barazanar da yankin ke fuskanta.
Islamabad ta jima da ta ke takun tsaka da manyan kasashen duniya kan makamanta masu linzami da na nukiliya.
Islamabad ta gudanar da gwaje-gwajen nukiliya na farko a cikin 1998 don mayar da martani ga Indiya kuma tun daga lokacin ta kera manyan makamai masu linzami masu karfin nukiliya.