Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara.
Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa Peshawar.
Manufar garkuwan dai ita ce neman gwamnatin Pakisatn ta bawa yankin Baluchistan na kasar Pakisatan yencin kanta a matsayin kasa mai zaman kanta.
Labarin ya ce yan bindigan sun ta da nakiya ne suka lalata layin dogon, kafin su tilastawa Jirgin tsayawa.
Ya zuwa yanzu dai yan bindigan sun kashe mutane 3 daga cikin har da direban jirgin.