OIC, Ta Bukaci A Hukunta Wadanda Suka Kai Hari Kan ‘Yan Hijira A Rafah

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi Allah wadai da harin da sojojin Isra’ila suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira a birnin

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi Allah wadai da harin da sojojin Isra’ila suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Kungiyar na mai bayyana harin a matsayin wani mummunan kisan kiyashi, inda ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya dauki nauyin da ya rataya a wuyansa na tilastawa gwamnatin ta dakatar da irin wannan tsokana.

Kungiyar ta OIC mai mambobi 57 a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta ce dole ne a hukunta wadanda suka kai harin a sansanin na Rafah tare da fuskantar dokokin kasa da kasa.

“OIC ta sake sabunta kiran da take yi ga kasashen duniya, musamman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da su dauki nauyin da ya rataya a wuyanta na tilastawa Isra’ila, aiwatar da umarnin kotun kasa da kasa na dakatar da wannan cin zarafi na Isra’ila cikin gaggawa.”

Rafah da ke kan iyakar Gaza ta kudu da Masar, tana da kimanin Falasdinawa miliyan guda da suka rasa matsugunansu da suka yi gudun hijira daga sauran yankunan da aka yi wa kawanya a yakin da Isra’ila ke yi.

Kisan Rafah ya zo ne kwanaki biyu bayan da kotun kasa da kasa (ICJ) ta umurci Isra’ila da ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a yankin.

A halin da ake ciki, babban jami’in jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya caccaki firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu saboda ikirarin cewa harin da aka kai ta sama kan  Rafah “kuskure ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments