Search
Close this search box.

OIC: Dole Ne Isra’il Ta Dakatar Da Kisan Kiyashi A Gaza Ba Tare Da Sharadi Ba

A taron musamman da kungiyar kasashen Musulmi ta OIC ta yi a birnin Jiddah na Saudiyya ta yi kira da a kawo karshen yakin Gaza

A taron musamman da kungiyar kasashen Musulmi ta OIC ta yi a birnin Jiddah na Saudiyya ta yi kira da a kawo karshen yakin Gaza ba tare bata loakci, kuma ba tare da wasu sharudda ba.

Taron na kungiyar kasashen musulmi an yi shi ne a matakin ministocin harkokin waje, an kuma kawo karshensa da fitar da bayani wanda bayan bukatar ganin an kawo karshen yakin na Gaza, ya kuma yi kira da a bude iyakoki da Gaza domin shigar da kayan agaji.

Wani sashe na bayanin bayan taron ya yi gargadi akan hatsarin da yake tattare da barin HKI tana cigaba da aikata manyan laifuka akan mutanen Gaza ta hanyar yi musu kishin kiyashi.

Ministocin harkokin waje na kasashen musulmin sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki a aikace, domin yin matsin lamba akan HKI ta kawo karshen laifukan da take tafkawa akan mutanen Gaza.

Jamhuriyar musulunci ta Iran ce dai ta bukaci a yai wannan taron na musamman akan Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments