Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani sabon kuduri da bai dace da Iran ba.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan, a gefen taron kasa da kasa mai taken ‘’yancin kasa da kasa na fuskantar barazana a martanin ga kungiyar tarayyar Turai a sahun gaba (Faransa, Burtaniya, da Jamus) da suka gabatar da wani sabon kuduri kan Iran a taron Kwamitin Gwamnonin IAEA na mako mai zuwa.

“Ina fatan Tarayyar Turai za ta yi aiki da hankali kuma ba za ta gabatar da kudurin a hukumance ba, amma idan ta yi, Iran za ta yi gyara na asali ga manufofinta,”.

Mista Gharibabadi ya kara da cewa kasashen Turan uku sun janye daga tattaunawa da duk wasu hanyoyin diflomasiyya da Iran ta hanyar kaddamar da tsarin nan na snapback, wanda ya sake dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran bisa fakewa da shirin nukiliyarta na zaman lafiya.

Ya kuma soki wasu kasashe saboda shirunsu, ko ma goyon bayansu, game da ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yuni.

“Duk da haka, Iran ta nuna kyakkyawan fata kuma ta ci gaba da hulda  da IAEA game da cibiyoyin da ba a kai wa hari ba,” in ji shi.

Jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa bayan dawo da tsarin ne da ake kira snapback, Iran ta yi watsi da Yarjejeniyar Alkahira, wacce ta tanadi hulda da IAEA.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments