Nijar ta yi Tir da kasashen ketare kan tada zaune tsaye a Sahel

Firaministan Nijar Mahaman Lamine Zein ya yi Allah wadai da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel. Lamine Zein,

Firaministan Nijar Mahaman Lamine Zein ya yi Allah wadai da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel.

Lamine Zein, ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar da a zauren babban taron MDD karo na 80 dake gudana a birnin New York.

Nijar ta kuma yi Allah wadai da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza, da kuma hare haren Isra’ilar kan Iran da Qatar, da kuma yadda ake nuna halin ko in kula game da rikicin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da Sudan dama yankin Sahel tare da hadin bakin wasu manyan kasashen yamma a nahiyar Afrika.

Fira ministan na Nijar, Ya kuma kara da cewa gwamnatin Nijar da takwarorinta na Burkina da Mali, a sun sha bayyanawa duniya shaida ta yadda wasu mayan kasashen yamma ke da hannu wajen tada zaune tsaye a kasashen kawancen AES ta hanyar goyan bayan ‘yan ta’adda.

Ya yi Allah-wadai da Faransa da faransa kan goyan bayan ayyukan ta’addaci a yankin Sahel musamman a Nijar tun bayan janye sojojinta a 2023, ta hanyar bai wa ‘yan ta’addan bayanai, horo, kudade da kuma kayan aiki.

Haka kuma ya zargi faransa da kawo cikas ga duk wani shiri na ci gaba da kin amincewa da duk wani shiri na Nijar a gaban hukumomin lamuni na kasa da kasa irinsu bankin ci gaban Afrika, Asusun bada lamuni na duniya IMF, da bankin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted