Nigeria Ta Yi Gargadi Ga ‘Yan Kasar Da Su Kaucewa Shiga Cikin Yakin Da Ake Yi A Tsakanin Kasashen Waje

Gwamnatin kasar ta Nigeria ta gargadi ‘yan kasar tata da su kaucewa shiga cikin yake-yaken da a ke yi a kasashen waje, bayan da aka

Gwamnatin kasar ta Nigeria ta gargadi ‘yan kasar tata da su kaucewa shiga cikin yake-yaken da a ke yi a kasashen waje, bayan da aka sami wasu rahotanni da suke nuni da cewa da akwai ‘yan kasar da aka yaudare su aka shigar da su cikin yakin kasashen Rasha Ukiraniya.

Wannan sanarwar dai ta fito ne daga ma’aikatar harkokin wajen Nigeria, wacce ta kunshi nuna damuwa akan yadda ‘yan kasar suke shiga cikin fadace-fadace na kasashen waje.”

Sanarwar ta ma’aikatar harkokin wajen Nigeria ba ta ambaci sunan kasar Rasha ko Ukiyaniya ba.

Sai dai rahotanni da dama suna nuni a cewa da akwai ‘yan kasashen Afirka masu yawa da aka yaudara aka shigar da su cikin aikin soja, bayan da aka yi musu alkawullan samun kudade da dama.

A wani rahoto da kafar “All Eyes on Wagner” mai bincike akan yakin Rasha da Ukiraniya ta fitar a makon da ya shude, ta ce da akwai ‘yan Nigeria 36 da Rasha ta shigar da su a cikin sojojinta,suna yaki da kasar Ukiraniya,kuma an kashe 5 daga cikinsu a filin daga.

 Shi kuwa kamfanin dillancin labarun AFP ya fitar da wani rahoto da a ciki ya tattara bayanai daga ‘yan kasar Kenya da su ka yi yaki a filin daga da Ukiraniya.

Mutanen dai sun je kasar Rasha, ne inda aka tilasta musu sanya hannu akan wata yarjejeniya mai dungu da ba su fahimce ta ba, da ta kare da kai su filin dagar yaki da Ukiraniya.

Shi ma shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin akan yadda za a mayar da ‘yan kasar da suke yaki  zuwa gida.

Kasar Ukiraniya ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta bayyana cewa; da kawai mutane 1,436 da su ka fito daga kasashe 36 na Afirka wadanda suke yaki a cikin sojojin Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted