Nigeria: A cikin Shekara Daya Masu Garkuwa Da Mutane Sun Karbi Naira Biliyan 2.57

Jaridar “Daily Trust” ta Nigeria ta  dauki wani rahoto na na hukumar tattara bayanan sirri ta SBM dake cewa, masu garguwa da mutane a Nigeria

Jaridar “Daily Trust” ta Nigeria ta  dauki wani rahoto na na hukumar tattara bayanan sirri ta SBM dake cewa, masu garguwa da mutane a Nigeria sun karbi naira biliyan 2.57 daga watan Yuli na 2024 zuwa Yuni na 2025.

Rahoton wanda aka aka fitar a ranar 19 ga watan Disamba 2025 da kuma ya dauki taken: “Shekara Mai zuwa A Matakin Sauyi” ya yi nazari akan sauye-sauye na tattalin arziki da siyasa a cikin nahiyar ta Afirka a shekarar nan ta 2025 mai karewa, sannan kuma ya bayyana cewa a cikin watanni 12 masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya su kudaden da su ka kai naira biliyan 84,amma an biya su wani kaso daga cikin kudaden.

Rahoton na kungiyar SBM ya kuma ce; Alkalumma suna nuni da cewa garkuwa da mutane a Nigeria yana kara kazanta, da zama wata bakar sana’a da ake samun kudade,alokaci daya yana nuni da raunin gwamnati a cikin yankunan karkara da tabarbarewar harkokin tsaro.

Wani sashe na rahoton ya ce mutanen da aka sace sun kai 4,722 a hare-hare da aka kai har sau 997 a wannan tsakanin da aka mabata. Haka nan kuma an kashe mutane fiye da 762 a hare-haren da suke da alaka da masu garkuwa da mutane.

Hukumar ” SBM ” tana aikin tattara bayanai ne masu alaka da tsaro a yammacin nahiyar Afirka.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted